Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia: Jammeh ya bukaci Kotun Koli ta hana a rantsar da Barrow

Lauyan da ke kare shugaban Gambia Yahya Jammeh ya shigar da bukata a kotun Koli domin ganin ta hana a rantsar da Adama Barrow da ya lashe zaben shugaban kasar.

Yayha Jammeh na Fuskantar Matsin lambar ya mika mulki bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa
Yayha Jammeh na Fuskantar Matsin lambar ya mika mulki bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa Photo: GRTS via AFP
Talla

Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 yana shugabanci a Gambia ya ki amincewa da sakamakon zaben watan Disemba da ya sha kaye.

Rahotanni kuma sun ce lauyan Shugaban ya bukaci Kotun Koli ta hana a rantsar da Barrow a ranar 19 ga watan Janairu har sai an kamala shari’a.

Amma a cikin wata sanarwa, zababben shugaban na Gambia Adama Barrow ya ce babu wanda zai hana a rantsar da shi kamar yadda doka ta tanada.

“Wanda ya lashe zabe zai yi shirin bikin rantsuwa wanda kuma ya fadi ya ruga kotu, haka doka ta ce da babu wani dan Gambia da zai musanta” a cewar Barrow.

Jammeh dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya musamman Najeriya da ke jagorantar kasashen yammacin Afrika da ke shiga tsakanin rikicin kasar.

Najeriya ta bude kofar ba Jammeh mafaka idan har ya sauka cikin ruwan sanyi.

A yau Juma’a ne ake sa ran tawagar ECOWAS da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke jagoranta za su koma Gambia domin tattaunawa da bangarorin siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.