Isa ga babban shafi
Gambia

Adama Barrow zai gana da Shugabanni Afrika a Mali

Zababben shugaban kasar Gambia Adama Barrow zai gana da shugabanni da ke halartar taron kasashen Afrika da Faransa a birnin Bamako na Mali, taron da a yanzu ya karkata wajen gani ya kawo karshan rikicin siyasar Gambia.

Zababben Shugaban Kasar Gambia Adama Barrow
Zababben Shugaban Kasar Gambia Adama Barrow Photo: Seyllou/AFP
Talla

Shugaban Faransa Francois Hollane zai gana da Barrow kafin daga bisani ya zauna da shugabanni yammacin Afrika kan makomar Gambia.

Wannan na zuwa ne bayan Tawagar Ecowas ta gana da Yahya Jammeh wanda ke nuna turjiya mika mulki idan wa’adinsa ya cika.

Kungiyar kasashen Afrika, AU, ta ce daga ranar 19 ga watan Janairu za ta dai na mu’amala da Yahya Jammeh a matsayin Shugaban Gambia, ranar da wa’dinsa ke cika.

Wata sanarwa da Kwamitin tsaro a Majalisar ta fitar bayan zaman tattaunawa a birnin Habasha, ta gargadi matsalolin da ka iya biyo bayan turjiya da Jammeh ke nunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.