Isa ga babban shafi
Gambia- Ecowas

Shugaban Najeriya Buhari na kasar Mali don warware rikicin Gambia

Shugabannin kasashen Yammacin Africa dake kokarin warware rikicin siyasar Gambia tare da mutumin da ya lashe  zaben kasar Gambia Adama Barrow na kasar Mali yanzu haka, inda ake sa ran za su tattauna batun takaddamar.

Shugaban Gambia Yahya Jammeh tare da shugabannin kasashen yammacin Africa da suka kai masa ziyara ta farko
Shugaban Gambia Yahya Jammeh tare da shugabannin kasashen yammacin Africa da suka kai masa ziyara ta farko Nigeria president Twitter account
Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne dai ke jagorancin ayarin shugabannin uku dake wannan kokarin sulhu.

Tun watan jiya tsohon Shugaban Ghana John Dramani Mahama tare da Shugaban Liberia Uwargida Ellen Johnson Sirleaf  da Muhammadu Buhari na Najeriya ke ta kokarin ganin sun shiga tsakani dangane da rikicin  Gambia.

A wani labarin, kasashen dake cikin kungiyar kasashen yammacin Africa 15 sun amince za su nemi izinin komitin sulhu na MDD domin a tura Dakaru zuwa  Gambia muddin shugaba Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan wa'adin sa.

Jakadan MDD Mohammed Ibn Chambas ya fadi cewa ayarin  shugabannin kasashen yammacin African da suka sauka tun  jiya a Banjul sun tafi shaidawa Yahya Jammeh ne cewa yayi hattara.

Ya ce suna bukatar ganin ya mika mulki ga wanda ya lashe zaben wato Adama Barrow ba tare da wani jinkiri ba idan wa'adin sa ya cika.

Tuni dai Kungiyar Tarayyar Africa ta sanar da cewa daga ranar 19 ga wannan wata ba zata sake muamulla da Yahya Jammeh ba a matsayin shugaban Gambia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.