Isa ga babban shafi
Gambia

Majalisar Gambia ta tsawaita wa’adin Jammeh

Majalisar dokokin kasar Gambia ta amince shugaba Yahya Jammeh ya ci gaba da mulki har tsawon watanni uku, a yayin da ake shirin rantsar da Adama Barrow da ya lashe zaben kasar da aka gudanar a watan Disemba.

Dubban Mutanen Gambia na tserewa zuwa Senegal
Dubban Mutanen Gambia na tserewa zuwa Senegal REUTERS
Talla

Majalisar kuma ta amince da dokar ta-bacin da shugaba Jammeh ya kafa ta kwanaki 90.

Matakin wanda aka sanar a kafar telebijin din kasar zai kara tayar da hankalin ‘Yan Gambia da kuma kasashen duniya, musamman barazanar da ECOWAS ta yi na amfani da karfin soji domin tilastawa Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow.

A yau ne wa’adin Jammeh ke kawo karshe a matsayin shugaban Gambia bayan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Disemba.

Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta ce babu abin da zai hana a rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasar Gambia, duk da shugaba Yahya Jammeh ya yi biris da matsin lambar shugabannin kungiyar.

ECOWAS ta ce za a rantsar da Barrow a wani yanki na Gambia ba lalle sai Banjul ba fadar gwamnatin kasar, matakin da ke nuna za a samu hedikwatar gwamnati biyu a kasar.

Ministan harakokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa RFI cewa Adama Barrow ne duniya ta sani a matsayin halattaccen shugaban Gambia wanda za a iya rantsar da shi a ofishin jekadancin Gambia a Senegal.

Rahotanni sun ce yanzu haka Najeriya na shirin tura dakaru 200 a Gambia inda tuni jiragen ruwan yakinta suka nufi kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.