Gwamnatin Libya ta sanar da mallakar Sirte a hukumance
Gwamnatin hadin kan Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da kawo karshen ayyukan sojinta a birnin Sirte, bayan samun nasarar kakkabe mayakan IS daga cikinsa.
Wallafawa ranar:
Sai dai kuma Firaministan kasar Fayez al-Sarraj yayi gargadin cewa hakan ba yana nufin sun kawo karshen yaki da mayakan na IS bane.
Sojin Libya sun shafe watanni takwas kafin samun wannan nasara, inda a ranar 5 ga watan Disamba sojin kasar, suka sanar da karbe ikon birnin na Sirte daga hannun kungiyar IS, wanda ya zamo tungar kuniyar mafi karfi kuma ta karshe a kasar.
Kwace birnin Sirte, mahaifar tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi daga mayakan IS, babban koma baya ne garesu, duba da murkushe su da ake cigaba da yi a kasashen, Syria da Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu