Isa ga babban shafi
Libya

Sojin Libya sun kwace birnin Sirte daga mayakan IS

Sojin da ke biyayya ga gwamnatin hadaka ta Libya, wadanda kuma ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, sun samu nasarar kwace birnin Sirte daga karkashin ikon mayakan IS.

Sojin da ke biyayya ga gwamnatin hadin kai ta Libya
Sojin da ke biyayya ga gwamnatin hadin kai ta Libya Reuters/路透社
Talla

Kakakin rundunar sojin Libya Reda Issa, ya tabbatar da samun nasarar a wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Issa ya ce rayukan sojoji masu biyayya da dama sun salwanta yayin fafutukar ganin sun kwato birnin na Sirte da ke a matsayin tunga mafi karfi ta mayakan na IS a Libya.

Wani mai Magana da yawun babban asibitin da ke garin Misrata, Akram Glawan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, akalla sojin Libya 711 suka rasa rayukansu, yayin yakar mayakan IS cikin watanni 7 da aka aka kwashe ana yakin kwato birnin da ya kasance cibiyar IS a Libya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.