Isa ga babban shafi
Libya

Libya za ta fara amfani da tashoshin mai da 'yan tawaye suka mika mata

Hukumomin Kasar Libya sun sanar da cewar za’a fara fitar da man kasar daga tashoshi biyu daga cikin 4 da Yan tawaye suka mikawa Gwamnatin hadin kan kasar.

Shugaban Gwamnatin hadaka ta Libya Fayez Seraj
Shugaban Gwamnatin hadaka ta Libya Fayez Seraj REUTERS
Talla

Shugaban kamfanin Mustafa Sanalla yace za’a fitar da man ne daga tashoshin Zuwaytina da Ras Lanuf dan ganin kasar ta samu kudaden shiga.

Kasar Libya na fitar da ganga 600,000 kowacce rana, amma Sanalla yace nan da makwanni zasu karu zuwa ganga 950,000 kowacce rana.

Masu sharhi na kallon dawo da fara fitar da mai daga tashoshin da ‘yan tawaye suka mikawa gwamntin Libyan a matsayin wani karin matakin ga cigaban kasar bayan barkewar rikici a shekarar 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.