Isa ga babban shafi
Ghana

Mahama na son lashe zaben Ghana

A yayin da al'ummar Ghana ke shirin kada kuri’a a zaben shugabancin kasar a gobe , shugaba mai ci John Mahama ya bukaci lashe wani wa’adin shakeru hudu don habbaka tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama  da abokin hamayyarsa and Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da abokin hamayyarsa and Nana Akufo-Addo AFP/Wikimedia CC
Talla

A yayin rufe yakin neman zabensa a babban birnin Accra, shugaba Mahama da ke fuskantar babban kalubale a zaben, ya bukaci dubban magoya bayansa da su mara masa baya, in da ya ke tunatar da su irin ayyukan da ya yi musu na ci gaba.

To sai babban abokin hamayyarsa, Nana Akufo-Addo ya soki yadda shugaban ya tafiyar da mulkin Ghana, musamman kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma jefa al’umma cikin tsananin rayuwa.

Hankula dai za su fi karkata ne kan Mahama da Akufo-Addo daga cikin mutane bakwai da ke neman kujerar shugaban kasa a wanan karon.

Tun daga shekarar 1992, kasar Ghana dai ta gudanar da zabukan shugaban kasa a karkashin Demokradiyya cikin kwanciyar hankali, yayin da shugaba Mahama ke fatan gudanar da zaben na bana ba tare da hatsaniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.