Isa ga babban shafi
Habasha

Dala miliyan 200 don hana Habashawa zuwa cirani

Bankin Zuba jarin kasashen Turai yace zai rantawa kasar Habasha Dala miliyan 200 dan gina sansanin masana’antu biyu da zasu baiwa baki ‘yan cirani 30,000 aiki a wani yunkuri na hana su tsallakawa zuwa Turai.

Yan cirani dake kokarin shiga kasashen Turai.
Yan cirani dake kokarin shiga kasashen Turai. REUTERS/Alessandro Bianchi/Files
Talla

Bankin yace bakin 30,000 na daga cikin 100,000 da za’a samarwa aikin yi baki daya a karkashin wani shiri da zai ci Dala miliyan 500.

Bankin Duniya da Gwamnatin Birtaniya da kuma wasu kasashen Turai zasu bada sauran kudin da za’ayi aikin.

Akalla baki 743,000 tare da masu neman mafakar siyasa ke neman hanyar zuwa Turai daga kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.