Isa ga babban shafi
Habasha-MDD

Habasha na Bukatar tallafin dala milyan 500 domin kawar da Yunwa

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Habasha na bukatar tallafin akalla dala miliyan 500 don Sawaka matsalar da fari ke haifarwa a kasar kafin watan Afrilu.

AFP PHOTO/GIANLUIGI GUERCIA
Talla

Habasha da ke gab da fadawa cikin yanayin karancin abinci kamar yadda ta taba fuskanta a baya cikin shekara ta 1984 sakamakon karancin ruwan sama da yaki da ya kai ga rasa rayuka sama da miliyan 1 a kasar, yanzu sama da mutane Miliyan 10 ke fuskantar barazanar matsanancin yunwa

Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce Duk da cewa akwai zaman lafiya yanzu a kasar da kuma habbakar tattalin arziki, akwai bukatar taimakawa kasar a fannin noma domin magance matsalar da karancin ruwan sama ka iya haifarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.