Isa ga babban shafi
Habasha

Sama da mutane Miliyan 7 ke fama da yunwa a Habasha

Kungiyoyin bayar da agaji a kasar Ethiopia wato Habasha, sun ce akalla mutane Milyan 7 da rabi ne ke fama da yunwa a kasar, sakamakon karancin ruwan sama da aka fuskanta a daminar bana.

Aikin gona a Habasha
Aikin gona a Habasha Mike Goldwater/Getty Images
Talla

Tun cikin watan agustan da ya gabata ne dai Majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa yawan wadanda ke fama da yunwa a kasar sun kai miliyan hudu da rabi, to sai dai sabbin alkalumman da kungiyoyin agaji na kasar da kuma kasashen ketara suka fitar na nuni da cewa adadin ya ninka zuwa milyan 7 da dubu dari biyar.

Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar ya ce matukar dai ba a dauki matakan da suka wajaba ba, to kafin karshen shekarar badi, yawan mabukata a kasar zai kai milyan 15, wato fiye da wadanda ake da su a kasar Syria a yau.

Ita ma dai hukumar kula da kananan yara ta Majalisar dinkin duniya wato Unicef, ta ce yanzu haka akwai kananan yara sama da dubu 300 wadanda yunwa ta tagayyara su a kasar ta Ethiopia.

Ethiopia ko kuma Habasha ita ce kasa ta biyu mafi yawan al’umma a Afirka, kuma ta yi iyaka da kasashe da dama da ke fama da rikici-rikice, kamar Somalia inda ake da wasu dimbin mutane da ke fama da rashin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.