Sauran kiris ayi bankwana da goggon biri a Congo
Gwamanatin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo tayi shelara cewar saura kiris a rasa garken goggon birin da ya rage a cikin kasar saboda yadda ake kashe su inda tace hakan barazana ce ga dabbobin ganin adadin gogon birin da ake da su basu wuce 5,000 a duniya ba.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da namun daji ta duniya tace yanzu haka adadin gogon birin da ake da su basu wuce 5,000 a duniya ba.
Inger Anderson, Darakta Janar na hukumar kula da gadun dajin yace yadda ake farauta da kuma sassare dajuka na tsawon shekaru sun yi sanadiyar rasa kashi 70 na goggon birin.
Jami’in yace duk da yake an haramta kashe wadanan dabbobin, amma ana ci gaba da hallaka su ba tare da kaukautawa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu