Isa ga babban shafi
Sudan Ta Kudu

UNICEF ta damu da rikicin Sudan ta kudu

Hukumar UNICEF da ke tallafawa yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda ake tilastawa kananan yara shiga aikin soji a kasar Sudan ta kudu da ake fargabar cewar tana iya fadawa cikin wani sabon yakin basasa.

Dubban Mutane rikicin Sudan ta kudu ya raba da gidajensu
Dubban Mutane rikicin Sudan ta kudu ya raba da gidajensu Beatrice Mategwa/United Nations Mission in South Sudan (UNMISS)
Talla

Ganin yadda rikicin siyasar Sudan ta kudu ke ci gaba da bijirewa duk hanyoyin samun sulhu da kuma kafa gwanatin da kowane bangare zai amince, hukumar UNICEF ta bayyana damuwa kan halin da kananan yaran kasar suka samu kansu.

Mataimakin Daraktan hukumar Justin Forsyth ya ce yara kanana 16,000 aka tilastawa shiga aikin soji daga watan Disamba na shekarar 2013 da aka samu barkewar yakin basasa a kasar tsakanin ‘Yan Tawayen Riek Machar da sojojin gwamnatin Salva Kiir.

Forsyth ya ce fatar da suke da shi ga yaran da ke wannan sabuwar kasa, na ci gaba da dakushewa ganin yadda zaman lafiya ya gagara, da kuma yadda kasar ke fuskantar wani sabon tashin hankali na kokuwar mulki.

Daraktan ya ce yanzu haka rabin yaran kasar ba su zuwa makaranta, wanda hakan shi ne mafi yawa a duniya, abinda ke ba ‘Yan Tawayen damar tilasta wa yaran daukar makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.