Mutanen Sudan ta kudu na mutuwa saboda Yunwa
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace dubban mutane na rasa rayukansu sakamakon masifar yunwa a kasar Sudan ta Kudu, yankin da ake tafka yaki, tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawaye.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta roki bangarorin da ke rikici su su bari a shigar da kayan jinkai ga mabukata
Rahoton yace mabukata abinci cikin gaggawa sun kai dubu arba’in don lamarin ya kai inda ya kai.
A cewar rahoton lamarin na kara muni kullum domin kashi dubban mutanen kasar na cikin mawuyacin hali.
A 2013 ne rikici ya barke a Sudan ta kudu bayan shugaban kasar Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Reik Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.
Tun a lokacin dakarun da ke biyayya ga shugabannin biyu ke gwabza fada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu