Isa ga babban shafi
South Sudan-Sudan

Sudan ta bude iyakokin ta da Sudan ta Kudu

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir ya bayar da umurnin bude kan iyakokin kasar da Sudan ta Kudu, bayan rufe su a 2012 sakamkon rikici tsakanin kasashen biyu da ya biyo bayan ballewar Sudan ta kudu daga ikon gwamnatin Khartoum.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Matakin bude kan iyakokin na Sudan na zuwa ne bayan shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya umurci dakarun shi su janye daga kusa da kan iyaka da Sudan.

A cikin sanarwar da ya fitar shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir ya bukaci daukar dukkanin matakan da suka dace na aiwatar da matakin.

Tun ballewar yankin Sudan ta kudu daga Sudan a 2011 kasashen biyu ke rikici tsakaninsu kan wasu yankuna masu arzikin mai.

Babu kuma wata cikakkiyar alaka a yanzu tsakanin gwamnatin Khartoum da juba tun ballewar Sudan ta kudu daga Sudan a 2011 karkashin yarjejeniyar da suka amince ta kawo karshe yakin basasa.

Kuma tun a lokacin sun kasa samun jituwa kan batutwa da dama da suka hada da kan iyaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.