Akalla mutane dubu 50 sun mutu a yakin Sudan ta Kudu
Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, akalla mutane dubu 50 ne suka rasa rayukansu a yakin basasar Sudan ta Kudu, adadin da ya ninka wanda kungiyoyin agaji suka bayar sau biyar.
Wallafawa ranar:
Rikicin siyasa tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa, Riek Machar, shi ne musabbabin barkewar yakin a watan Disamban shekara ta 2013.
Wani babban jami’in majalisar dinkin duniya ya shaida wa manema labarrai cewa, yakin ya haifar da ‘yan gudun hijira sama da miliyan 2 .
Sannan ya bayyana shakkunsa game da yiwuwar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da aka kulla a watan Agustan da ya gabata.
A watan jiya ne majalisar dinkin duniya ta ce, bangarorin da ke fada da juna a Sudan ta Kudu na kashe mutane tare da lalata kayayyakinsu duk da yarjejeniyar da Kiir da Machar suka rattaba wa hannu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu