Isa ga babban shafi
Sudan-UN

Ana sa ran soma tattaunawa a Sudan ta Kudu

Wata tawagar manyan jami’an ‘yan tawayen Sudan ta Kudu ta isa birnin Juba a wannan litinin, wata alama da ke tabbatar da cewa bangaren gwamnati da na ‘yan tawaye sun fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla a cikin wata agustan da ya gabata. 

Salva Kiir Shugaban kasar Sudan ta kudu da tsohon mataimakinsa Rieck Mashar
Salva Kiir Shugaban kasar Sudan ta kudu da tsohon mataimakinsa Rieck Mashar
Talla

Rahotanni sun ce tawagar ‘yan tawayen za ta tattauna ne da gwamnatin Salva Kiir a game da batun kafa sabuwar gwamnatin hada-ka, to sai dai babu Rieck Machar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran ‘yan tawayen a cikin wannan tawaga.

Ranar 15 ga watan Disemba Shekarar 2015 aka cika shekaru biyu da barkewar rikici a kasar Sudan ta kudu tsakanin dakarun gwamnatin Salva Kiir da masu biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Rikicin kasar ya soma ne bayan shugaba Kiir ya zargi Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa, daga baya kuma rikicin ya rikide ya koma na kabilaci tsakanin kabilun shugabannin biyu.

Sau takwas bangarorin biyu na rusa yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince a Addis Ababa domin kawo karshen rikicin kasar.

Sama da mutane 50,000 aka kiyasta sun mutu a rikicin, yayin da kuma rikicin ya raba sama da mutane Miliyan biyu da rabi da gidajensu.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane Miliyan hudu da rabi ke bukatar taimakon abinci a Sudan ta kudu a yanzu haka.

Kokarin da aka yi na kafa gwamnatin hadin kai tsakanin bangaren gwamnatin Salva Kiir da Riek Machar ya faskara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.