Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Hatsarin jirgin sama ya hallaka mutane kusan 40 a Sudan ta Kudu

Wani jirgin saman daukar kaya da kasar Rasha ta kera, ya yi hatsari jim kadan da tashin sa daga filin jiragen sama dake Juba babban birnin Sudan ta kudu, inda mutane akalla 36 suka rasa rayukansu.

Akalla mutane 36 ne suka rasu a hatsarin jirgin Sudan ta kudu
Akalla mutane 36 ne suka rasu a hatsarin jirgin Sudan ta kudu Reuters/AU UN IST Photo/Tobin Jones
Talla

Wadanda hatsarin ya yi sanadiyar ajalinsu sun hada da na cikin jirgin da kuma wasu jama’a dabam da ke kan doran kasa.

To sai dai daya daga cikin ma’aikatan jirgin da wani jariri sun tsira a hatsarin kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar Sudan ta kudu, Ateny Wek Ateny ya shaida wa manema labarai.

Ateny ya kara da cewa da yiwuwar jirgin ya kwaso mutane 20 da suka hada da ma’aikatansa da kuma fasinjoji amma za su gudanar da bincike domin sanin hakikanin adadin mutanen da ke cikinsa.

A cewar Ateny ba su da masaniya game da yawan mutanen da lamarin ya shafe a doran kasa.

Wani jami’in 'yan Sanda ya bayyana cewa da yiwuwar adadin mamatan ya haura.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.