Majalisar Dinkin Duniya zata bincike Sudan ta Kudu
Majalisar Dinkin Duniya ta kadadmar da bincike kan harin da Yan Tawayen Sudan ta kudu suka kai wani otel dake Juba, inda suka kashe wani dan Jarida suka kuma yiwa mata fyade lokacin da aka fafata tsakanin su da sojojin gwamnati.
Wallafawa ranar:
Ana zargin sojojin Majalisar ne da kasa kai dauki dan kare fararen hular dake cikin wani otel da ake kira Hotel Terrain dake Juba duk da yake an shaida musu lokacin da fadan ya kazance.
Ban ki Moon ya bayyana takaicin sa dangane da zargin da aka yiwa sojojin samar da zaman lafiyar.
Majalisar dinkin Duniya ta sha zargin sojin gwamnati da bangaren 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki, lamarin da yake kara rura wutar rikici a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu