Isa ga babban shafi
Sudan

‘Yan tawayen Sudan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Sulhu

Babbar kungiyar ‘yan tawayen kasar Sudan ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiyar da kungiyar tarayyar Afrika ta shata domin kawo karshen yakin basasar tsawon shekaru da ta kwashe tana yi da gwamnatin Khartum, a yankunan Darfur, kogin Nilo da kuma Kurdufan ta kudu.

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan
Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar Jam’iyar national Congrès ta shugaban kasar Omar Hassan el-Bashir ta bayyana matukar farin cikinta dawannan abin farin ciki da ‘yan tawayen suka yi na saka hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar.

Dubun dubatar fararen hula ne dai, suka rasa rayukansu a yayin da wasu miliyoyi suka kauracewa gidajensu a shekarun da suka gabata, a wadanann yankuna inda kungiyoyin kabilu marasa rinjaye suka dauki makamai kan gwamnatin shugaba Albashir da larabawa zalla suka mamaye.

A lokacin tattaunawar da aka yi a cikin watan maris da ya gabata a birnin Adis Ababa na kasar Habasha ne, gwamnatin kasar Sudan ta sanya nata hannun kan yarjejeniyar zaman lafiyar, amma kuma sai babbar kungiyar ‘yan tawayen taki ta saka nata hannun bayan da ta nuna shakku kan wasu batutuwa da yarjejeniyar ta kunsa.

Bayan kwashe tsawon kwanaki ana tattaunawa a birnin na Adis Ababa, sai ajiya ‘yan tawayen ta saka nasu hannun, bayan samu tabbacin ci gaba da tattauna sauran batutuwan nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.