Isa ga babban shafi
Sudan

Mutane 100,000 sun fice Darfur

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane sama 100,000 suka gudu suka bar gidajensu a yankin Darfur na Sudan sakamakon wani sabon tashin hankalin da aka samu tun daga watan Janairun da ya wuce.

Daya daga cikin mutanen Yankin Darfur da rikici ya raba da gidajensu
Daya daga cikin mutanen Yankin Darfur da rikici ya raba da gidajensu REUTERS/Albert Gonzalez Farran/ys
Talla

Shugaban aikin samar da zaman lafiya Herve Ladsous ya sanar da haka a jawabin da ya ke yi wa kwamitin Sulhu, yana mai cewar matsalar ta fi kamari ne a Jabel Marra, inda ake ta samun hare haren sama.

Ladsous ya ce akalla mutane 138,000 suka fice yankin Jabel Marra da ke karkashin ikon ‘Yan tawayen SLA da Abdulwahid Nur ke jagoranta

Sai dai Jakadan kasar Sudan a Majalisar Omar Dahab Fadi ya musanta rahotan inda yace mutanen yankin da dama da fadan a baya ya sa suka bar gidajensu sun dawo, kuma yanzu haka suna noma.

Sama da mutane 300,000 Majalisar Dinkin Duniya ta kisyasta an kashe a rikicin Darfur tun a 2003.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.