Isa ga babban shafi
Madagascar

Gobara ta kashe mutane 38 a Madagascar

Gobara da ta auku a karshen mako ta yi sanadiyar mutuwar mutane 38, ciki har da yara kanana akalla 16, kamar yadda kakakin ‘yan sandan kasar Madagascar ya sanar.

Gobara a Madagascar
Gobara a Madagascar RFI/Sarah Tétaud
Talla

Lamarin ya auku ne a wani kauye da ake kira Ambalavato, Mutunen 38 da ta lakume rayukansu yan’uwan juna ne da ke liyafar bude sabon gidan wasu ma’aurata

Rahotanni na cewa maigidan baya gari a lokacin gobarar, sai dai kuma matarsa da ‘ya’yansa 6 sun rasa rayukansu, a yayin da yaronsu guda mai shekara 14 ya tsira da ransa.

Gobarar ta soma ne daga dakin da aka yi girki, kuma kafin jama’a su farga wuta ya mamaye ko’ina, al’amarin ya kara muni ganin hanyar fita daga gidan guda ne tilo, mutanen dake wajen gida sun yi kokarin kai musu dauki ba tare da samun nasara ba.

Daga cikin mutane 38 da suka mutu sha shida daga cikinsu kanana yara ne sai kuma yaro 1 da ya tsira da ransa.

Yankin na Ambalavato dake tsakiyar kasar ta Madagascar na yawan fama da matsalolin ‘yan fashi daya daga cikin dalilan da suka hana mahalarta liyafar komawa gida a ranar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.