Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Yaki ya sake barkewa a Sudan ta kudu

Yaki ya sake barkewa a Sudan ta kudu a yayin da aka yi musayar wuta tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaban ‘Yan tawaye kuma mataimakin shugaban kasa Riek Machar da kuma dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir.

Dakarun gwamnatin Sudan ta kudu.
Dakarun gwamnatin Sudan ta kudu. AFP Photo/Albert Gonzalez Farran
Talla

Rahotanni sun ce sama da mutane 150 aka kashe a musayar wutar da aka shafe kwanaki biyu ana yi a Juba babban birnin kasar.

Dakarun da ke biyayya ga Reik Machar sun ce dakarun gwamnati ne suka fara kai masu hari a Juba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an yi barin wuta da muggan makamai, kuma rikicin ya bazu a sassan Juba a yau Lahadi. Sannan rikici ya sa an rufe tashar jirgin sama a Juba yayin da jirage da dama suka dakatar da sauka da tashi.

Amurka ta gargadi ‘yan kasarta su rufe kansu a gida.

Sabon rikicin dai na nuna yarjejeniyar sulhu da aka cim ma a bara za ta rushe, wanda kasashen duniya ke ganin za ta kawo zaman lafiya a kasar bayan barkewar rikici a watan Disemban 2013.

Sabon rikicin na zuwa ne duka kwana guda bayan kasar ta cika shekaru 5 da samun ‘yanci daga Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.