Isa ga babban shafi
Masar

Wani Jirgin EgyptAir ya bata

Wani jirgin saman fasinjar EgyptAir mallakin kasar Masar ya bata bayan ya tashi daga birnin Paris na Faransa a cikin daren jiya dauke da mutane 66 a cikinsa.

Ana binciken Jirgin EgyptAir a Mediterranean
Ana binciken Jirgin EgyptAir a Mediterranean PASCAL PAVANI /AFP
Talla

Hukumomin Masar sun ce an daina jin duriyar jirgin ne a lokacin da ya shiga yankin arewacin kasar.

Jirgin ya tashi ne daga birnin Paris da misalin karfe 11 na daren jiya a hanyarsa ta zuwa birnin Al kahira.

Wani babban jami’I a kamfanin jiragen saman na EgytAir Ahmed Adel, ya ce jirgin wanda ya kamata ya sauka a birnin Alkahira da misalin karfi uku da mintuna 5 na safiyar yau Alhamis, ya bata ne ba tare da an samu wani sako ba ko kuma alamar cewa yana fuskantar wata matsala daga matukinsa ba.

Hukumomin Jirgin sun tabbatar da cewa akwai Faransawa 15 da kuma ‘yan asalin Masar 30 a cikin wannan jirgi da ya bata.

Akwai kuma ‘yan kasashen Birtaniya da Canada da Belgium da Portugal da Algeria da dusan da Chadi da Iraqi da Kuwait.

Shugaban Faransa Faransa Francois Hollande ya zanta ta wayar tarho da hukumomin Masar kan bacewar jirgin.

Tuni dai hukumomi a Masar da kuma kasar Girka suka aike da jiragen ruwa da kuma sojan ruwa domin fara bincike a kan tekun Mediterranean yankin da ake zaton a nan ne jirgin ya bata.

A ranar 31 ga watan Okotaban bara wani jirgin kasar Rasha dauke da mutane 224 ya tarwatse bayan ya tashi daga tashar Sharm El Cheikh, yayin da a ranar 29 ga watan Maris wani mutum da aka ce yana da tabin hankali, ya yi fashin wani jirgi da ya tashi daga birnin Alexandria zuwa kasar Cyprus dauka mutane 55 a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.