Faransa
Jirgin Air France ya yi saukar gaggawa a Kenya
Jirgin Faransa na air France ya yi saukar gaggawa a kasar Kenya bayan samun wani kunshi da ake zargin Bom ne a cikin jirgin da ke kan hanyarsa daga Mauritius zuwa Paris.
Wallafawa ranar:
Talla
Jirgin ya bar Mauricius ne a jiya da dare dauke da fasinja 459, zuwa misalin karfe 1 na dare kuma ya yi saukar gaggawa a filin jirgin Moi a Mombasa kasar Kenya.
Rahotanni sun ce jami’an kwance bom da sojojin sama sun dauki kunshin domin tantance ko bom ne.
Har yanzu rahotanni sun ce jirgin yana kasar Kenya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu