Isa ga babban shafi
France-Iran

Air France zai dawo da jigilar fasinjoji tsakanin Paris da Tehran

Bayan dakatar da jigilar Fasinjoji a shekara ta 2008 tsakanin biranen Paris da Tehran, a jiya talata kamfanin zirga-zirgar Jiragen saman Air France na kasar Faransa ya bayyana cewa a cikin watan Avrilun badi zai komawa jigilar fasinja tsakanin biranen 2.

Talla

Air France ya dauki wannan mataki ne sakamakon yarjejeniyar komawa huldar cinikayya da suka sanya hannu tsakanin Iran da manyan kasashen yammacin duniya.

A cikin wata sanarwa da kamfanin na Air France ya fitar a yau ya ce daga watan Avrilun shekara 2016 mai shirin kamawa zai komawa jigilar fasinjoji daga filin sauka da tashin jirgen sama na Charles de Gaulle da ke birnin Paris zuwa birnin Tehran na kasar Iran sau uku a mako.

A baya an dakatar da wannan zirga-zirga, saboda takunkuman kariyar tattalin arzikin da suka kakabawa kasar, bisa zarginta da kokarin samar da makaman nukliya mai makon makamashi.

Air Fransa ya ce zai kaddamar da zirga zirgar ne sau 3 a mako a ranakun Laraba Juma’a da kuma lahadi, bugu da Karin Kamfanin ya bayyana fatan da yake da shi na son fadada kansa a kasar Iran dake kan ganiyar farfado da tattalin arzikinta a duniya.

Nahiyar turai dai ta kasance a matsayin na hudu daga cikin jerin abukanan huldar cinakayya mai karfin da kasar jamhuriyar musulunci ta iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.