Isa ga babban shafi
Birtaniya-Rasha

Kakkabo jirgin Rasha aka yi a Masar- Birtaniya

Ministan Harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond yace akwai alamu mai karfin da ke tabbatar da kungiyar ISIS ce ta harbo jirgin Rasha a yankin Sinai na Masar wanda ya hallaka mutane 224.

Jirgin Fasinjan Rasha da ya tarwatse a yankin Sinai na Masar
Jirgin Fasinjan Rasha da ya tarwatse a yankin Sinai na Masar KHALED DESOUKI/RUSSIA'S EMERGENCY MINISTRY/AFP
Talla

Hammond wanda ke ziyarar aiki a Amurka domin tattaunawa da John Kerry ya ce gaskiyar al’marin zata bayyana idan masu bincike na kasashen Rasha da Masar sun kammala aikinsu.

Sakataren yace suna kyautata zaton cewar wani mai ra’ayi irin na kungiyar ne ya dasa bam din da ya tarwatsa jirgin amma ba Mayakan IS da ke Syria ba.

Kashi 90 cikin dari na Masu binciken hatsarin jirgin sun yi amannar cewa bam ne ya yi sanadiyyar fadowar jirgin a yankin Sinai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.