Taron shugabanin kasashe dake yakar Boko Haram a Abuja
Shugaban Faransa Francois Hollande ya samu isowa babban birnin tarrayar Najeriya Abuja,domin halartar taron kasashen dake yaki da kungiyar Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Wanan gangami na Abuja zai hada Shugabanin kasashe da za su yi bitar kokarin dama ci gaba da aka samu dangane da batun kawo karshen wannan kungiya ta Boko Haram .
Hollande Shugaban na Faransa da ya samu yada zango a jiya a kasar Afrika ta Tsakiya, a zantawarsa da hukumomin kasar ya sanar da matsayi faransa na cewa zata janye dakarun ta dake karkashin rundunar Sangaris, shugaban ya kuma tabbatar da cewa kasar sa zata ci gaba da kawo gudunmuwa dama horo kan batutuwan tsaro a kasashen Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu