Sojin Najeriya na horar da 'yan Boko Haram 800
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce, rundunar sojin kasar na horar da mayakan Boko Haram akalla 800 bayan sun tuba tare da ajiye makamansa domin karbar zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Rundunar dai na aikin sauya tunanin tsoffin mayakan ne domin su yi rayuwa mai inganci a tsakanin al’umma.
Hukumar ta NEMA ta ce, ana aikin wayar mu su da kai ne a karkashin wani shiri mai taken "Safe Corridor Initiative" kuma karkashin kulawar ofishin babban hafsan sojin kasar.
Wannan na zuwa ne a yayin da majalisaer dattawan kasar ke shirin amince wa da kudirin samar da hukumar farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya a ranar 25 ga wannan wata na mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu