Mutanen arewa maso gabashi za su samu tallafin N17,000
Daruruwan mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya za su samu tallafin kudi karkashin wani shirin hukumar samar da tallafin abinci ta duniya na raya mutanen yankin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gidaje akalla 500,000 za su samu tallafin kudi Naira dubu goma sha bakwai kowannensu a bana.
Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya Ambato shugaban hukumar agajin gaggawa ta Jihar Borno Ahmed Satomi yana cewa tuni gidaje dubu talatin da biyar suka karbi tallafin.
Rikicin boko haram dai ya sa miliyoyan mutane sun gujewa gidajensu baya ga dubbai da aka kashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu