Isa ga babban shafi
ICC

ICC na binciken rikicin Burundi

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague ICC ta ce, a wannan Litinin za ta fara binciken farko game da rikicin kasar Burundi.

Fatou Bensouda babban mai shigar da kara a cotun duniya ta ICC
Fatou Bensouda babban mai shigar da kara a cotun duniya ta ICC AFP
Talla

Babbar mai shigar ta kara ta Kotun Fatou Bensouda ta ce, tun daga watan Aprilun bara, ta ke bin abinda ke faruwa sahu da kafa a Burundi, lokacin da kasar ta tsindima cikin rikicin siyasa bayan shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da shirinsa na yin tazarce.

A cikin wata sanarwa da ta fitar Bensouda ta ce, sau da dama ta bukaci wadanda ke da ruwa da tsaki a rikicin Burundi da su kiyaye, inda ta gargade su cewa, za su iya fuskantar shari’a.

Ofishin Bensouda ya yi nazarin rahotannin da ke nuna yadda aka kashe mutane tare da azabtar da su baya ga rufe su a gidajen yari.

Rahotannin sun kuma bayyana yadda aka yi wa mata fyade da kuma tirsasa wa wasu kaurace wa muhallansu.

Rikicin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 430 yayin da aka rufe sama da dubu 3 a gidajen yari, sannan kuma kimanin mutane dubu 230 sun kaurace wa gidajensu, inda suka nemi mafaka a kasashe makwabta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.