Isa ga babban shafi
Burundi

An gano gawar mutane uku a Burundi

Mahakuntan Burundi sun sanar da gano wasu gawawwakin mutane 3 a birnin Bujimbura babban birnin kasar a yayin da wasu kwararu uku na Majalisar Dinkin Duniya suka fara gudanar da aikin binciken ayyukan take hakkin dan adam da aka gudanar a rikicin kasar.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

Kwararrun guda uku na Majalisar Dinkin Duniya zasu share tsawon kwanaki har zuwa 8 ga watan Maris suna gudanar da binciken da zasu gabatar da rahoton karshe ga zauren Majalisar a ranar 21 ga watan Maris.

Jim kadan bayan soma binciken nasu a jiya mahukumtan kasar suka sanar da gano wasu gawawwakin mutane uku da aka kashe aka kuma jefa a cikin rame guda a wata unguwar da ake yawan samun tashe tashen hankulla da ke arewa maso yammacin Bujumbura babban birnin kasar ta Burundi.

Hukumomin kasar sun zargi masu adawa da gwamnati da alhakin kisan mutanen uku.

Majiyar dai ta bayyana cewa daya daga cikin makasan da aka kama ne ya bayyanawa mahukuntan kasar kisan da suka yi ya kuma nuna masu inda suka binne mutanen 3 inda a halin yanzu ake ci gaba da binciken gano karin wasu mutanen da watakila aka kashe aka kuma binne ba tare da sanin hukumomi ba.

Burundi ta fada rikici ne tun lokacin da shugaba Pierre Nkunzixa ya bayyana aniyar sake tsayawa takarar shugabancin kasar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.