‘Yan gudun hijira na fama da yunwa a tafkin Chadi
Yunwa da tsoron harin kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko haram ya ritsa da su a Yankin tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
Florent Mehaule, jami’in aikin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a garin Baga Sola ya ce akalla ‘yan gudun hijira 110,000 ke rayuwa a sansanonin da ‘yan gudun hijira suka samarwa kansu a gabar ruwan tafkin Chadi da ya kewaye kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.
Jami’in yace duk da jami’an tsaron da ke kula da su ana samun hare hare nan da can abin da ke razana mutanen da ke sansanin.
Sannan ‘Yan gudun hijira na fama da yunwa a yayin da suke zaman zullumi da fargabar yiyuwar hare haren yan Boko Haram.
An dai taba kai hare haren kunar bakin wake a garin Baga Sola a watan Oktoba inda aka kashe mutane 41.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu