Isa ga babban shafi
Liberia

Hukumomin Liberia na Kwantar da Hankulan Jama'a Game da Sake bullar Cutar Ebola

Hukumomi a kasar Liberiya sun nemi jama'a da’a kwantar da hankula sakamakon sake bullar cutar Ebola a kasar, watanni biyu bayan da aka sanar da duniya cewa kasar ta yi bankwana da wannan cuta.

Wasu maaikata na Lafiya  a kasar Liberia cikin kayan kare kamuwa da cutar Ebola
Wasu maaikata na Lafiya a kasar Liberia cikin kayan kare kamuwa da cutar Ebola AFP PHOTO / DOMINIQUE FAGET
Talla

Mace da aka samu ta baya-bayan nan itace  mai shekaru 30 wadda ta mutu ranar Alhamis data gabata a Manrovia babban birnin kasar Liberia.

Babu dai Karin haske ko daga inda maccen ta kai kamu da wannan cuta mai saurin kashe mutane.

Mukaddashin Ministan Lafiya na kasar Tolbert Nyensuah ya bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.