Ebola: ‘Yan sanda sun yi arangama da Matasa a Saliyo
Mutane uku sun samu raunuka a wata tarzoma da ta barke tsakanin ‘Yan sanda da Matasa a kasar Saliyo bayan sun bukaci ‘Yan kasuwa su rufe shagunansu a garin Barmoi domin farautar masu dauke da cutar Ebola.
Wallafawa ranar:
Rikicin ya faru ne bayan mutuwar wata a yankin mai dauke da cutar Ebola. Kuma ‘Yan sanda na neman mutane sama da 40 da suka yi mu’amula da matar mai shekaru 22.
Matasa a garin sun farwa ‘Yan sandan ne bayan sun rufe shagunansu. Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsuhuwa tare da harba bindiga akan matasan.
Matasa uku ne aka sanar sun jikkata a arangamar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu