Isa ga babban shafi
Saliyo

An sake samun mutum na biyu mai cutar Ebola a Saliyo

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da samun wata Mata da ta kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo, mutum na biyu ke nan bayan sanar da kawo karshen cutar makon da ya gabata

Mutum na biyu ya kamu da Ebola a Saliyo
Mutum na biyu ya kamu da Ebola a Saliyo KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

Tarik Jasarevic, mai Magana da yawun hukumar ya bayyana cewar wata mata mai shekaru 38 da ta kula da Marie Jalloh da ta mutu ranar 12 ga wata ce ta kamu da cutar.

Matar ‘yar uwa ce ga Marie Jalloh.

Yanzu haka kimanin mutane 150 ake kula da su wadanda suka yi mu’amula da Jalloh.

Wannan ya sa kasar ta sake bude sansanin kula da masu fama da cutar da aka rufe.

A makon da ya gabata ne hukumar lafiya ta sanar da kawo karshen Ebola a Afrika, bayan kawar da cutar a Liberia.

Tun a watan Nuwamba aka sanar da kawar da cutar a Saliyo amma yanzu Ebola ta tsake bulla a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.