Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Al Qaeda ta dauki alhakin kazamin harin Otel a Cote d'voire

Wata Kungiyar da ke da alaka da Al Qaeda ta dauki alhakin kai kazamin harin da ya hallaka mutane 16 a wani otel da ke gabar ruwan Grand Bassam a kasar Cote d’Ivoire.

Mayakan al-qaeda sun dau alhakin harin Otel din Etoile du Sud
Mayakan al-qaeda sun dau alhakin harin Otel din Etoile du Sud REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shaidun gani da ido sun ce maharan dauke da bindigogi da gurneti sun bude wuta kan masu yawon bude ido akasarin su ‘yan kasahsen Turai.

Shugaban kasar Cote d'Voire Alassane Ouattara ya ce an kashe mutane 14 tare da sojoji 2.

Rahotanni sun ce an dau tsawon dakikai 30 zuwa 40 ana harbe-harbe a wajen shakatawa da ake kira Etoile du Sud.

Tuni dai shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yi allawadai da harin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake kaddamar da hari a wajen shakatawa ba, ko a watan Janairu sai da aka hallaka mutane 30 a wani Otel da ke Burkina faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.