Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari-Falasdinu

Najeriya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayan sa na ganin an kafa kasar Falasdinu dan kawo karshen matsalolin da Falasdinawa ke fuskanta a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin da ya ke ganawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hammad al Thani, shugaba Buhari ya ce Najeriya na goyan bayan daukacin kudirorin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su wajen samun kasashe biyu tsakanin Israila da Falasdinu.

Buhari ya shaidawa Sarkin cewar Najeriya za ta hada kai da Qatar har sai ta ga Falasdinu ta samu biyan bukata.

Idan dai ba’a manta ba a shekarar da ta gabata, Najeriya taki kada kuri’ar goyan bayan Falasdinu a kwamitin Sulhu a karkashin shugabancin Goodluck Jonathan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.