Furgaban barkewar sabuwar rikici tsakanin Falasdinawa da Isra'ila
Tun ranar Assabar da ta gabata wasu garuruwa da ke gabar yammacin kogin Jodan, da kuma wasu unguwannin dake gabashin birnin Kudus ke arangama da matasan Falasdinawa da ke tunawa da zagayowar ranar ‘’Intifada’’ da aka Assasa gwagwarmayar Falasdinawa a shekarar 1987 da kuma shekarar 2000
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Intifadar dai ta soma ne, da jifar duwatsu da kwalaben ''aci-balbal'' daga matasan falasdinawa, a yayin da su kuma sojojin Isra'ila suka mayar da martani da harbin bindiga, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 48 wasu 150 kuma suka jikkata.
A jiya litinin dai wata sabuwar tarzomar ta kara barke a gabar yammacin kogin Jodan.
Intifada da ke nufin Bore da larabci, ko kuma yaki ta hanyar jifa da duwatsu da Falasdinawa ke yi, ya fara ne tun a shekarar 1987 sanadiyar wata babbar motar dakon kaya ta kasar Isra'ila da ta markade wata motar falasdinawa tare da kashe daukacin Falasdinawan 4 da ke cikin motar.
Wannan dai shine masomin farko na barkewar gwagwarmayar ta Intifada, neman yancin kan falasdinawa a yankunan da Isra'ila ta mamaye.
Hotunan da suka zagaya duniya na rashin imani da Isra'ila ta nuna a kan Falasdinawan dai, ya yi matukar tunzura wasu kasashe da kuma wasu kungiyoyin da ke hankoron kare hakkin dan adam na duniya a wancan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu