Isa ga babban shafi
EU

EU ta ja kunnen Isra'ila kan Falasdinawa

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta ja kunnen Isra’ila kan hare haren da ake kai wa Falasdinawa a yankunan da kasar ke ci gaba da mamaye wa a gabar yamma da kogin jordan. 

Wadansu jerin hare hare da aka kai yankin Gaza
Wadansu jerin hare hare da aka kai yankin Gaza REUTERS/Baz Ratner
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kisan wani jinjiri Bafalasdine a yau Juma’a.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci mahukutan Isra’ila su bi hanyoyin wanzar da zaman lafiya a yankunan Falasdinawa, lura da rikicin mamayar da kasar ke ci gaba da yi gabar yamma da kogin Jordan.

Babbar jami’ar diflomasiyar Turai ta fadi a cikin wata sanarwa cewa akwai bukatar bin hanyoyi na siyasa domin kawo karshen zubar da jini a rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Kuma matakin Isra’ila na sake gina sabbin matsugunai a yankunan Falasdinawa shi ya kara rura wutar rikici a gabar yamma da kogin Jordan.

Tuni kuma kungiyar ta EU ta yi allawadi da matakin gina sabbin gidajen da Isra’ila zata yi a yankunan Faladinawan, lamarin da ta ke ganin Isra’ila na yi wa kokarin da ake na sasanta rikicin gabas ta tsakiya karan tsaye.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.