Isa ga babban shafi
FIFA

Falasdinawa za su yi wasan zumunci da Isra’ila

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Sepp Blatter yace za a yi wasan sada zumunci tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a birnin Zurich na Switzerland don taimakawa zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Sepp Blatter na gaisawa da Ofer Eini shugaban kwallon Isra'ila
Sepp Blatter na gaisawa da Ofer Eini shugaban kwallon Isra'ila REUTERS
Talla

Blatter wanda ya kai ziyara a Isra’ila ya ce Firaministan kasar Benjamin Netanyahu zai halarci filin wasan da Yahudawa za su buga wasa tsakaninsu da Falasdinawa.

Wannan na zuwa ne bayan Falasdinawa sun nemi FIFA ta kori Isra’ila a cikin mambobinta, saboda yadda Isra’ila ke yin tarnaki ga ci gaban ‘Yan wasan Falasdinawa
Tun a 1998 Falasdinawa suka samu wakilci a hukumar FIFA

Falasdinawa na adawa da yawan kungiyoyin Isra 'ila a yankunansu da ta mamaye a gabar yamma da kogin jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.