Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya da Bill Gates za su yaki Maleriya a Afrika

Gwamnatin Birtaniya tare da hadin guiwar attajirin Amurka Bill Gates sun sanar da matakin ware makudan kudade domin yakar zazzabin cizon sauro da ke barazana ga lafiyar al’umma yawanci a Nahiyar Afrika.

Attajirin Amurka  Bill Gates
Attajirin Amurka Bill Gates RFI/Didier Bleu
Talla

Ministan kudin Birtaniya George Osborne da Bill Gates sun sanar da ware kudi sama da dala biliyan hudu domin yakar Maleriya a cikin shekaru biyar.

Kudaden sun shafi gudanar da binciken da bayar da tallafi ga ayyukan magance zazzabin na Maleriya.

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace adadin mutane 438,000 suka mutu a 2015 sakamakon zazzabin Maleriya, kuma yawancinsu yara kanana ne ‘yan kasa da shekaru biyar mafi yawanci a Nahiyar Afrika.

Bangarorin biyu sun yi gargadin cewa matsalar za ta fi yin kamari zuwa shekarar 2020 idan har babu wani magani da aka samar.

A sanarwar da aka wallafa a Jaridar Times, Bill Gates da Birtaniya sun yi alkawalin kawar da Maleriya baki daya.

Wannan dai na zuwa ne bayan Bill Gates ya kaddamar da shirin ware kudade dala Miliyan 100 domin magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.