Afrika taTsakiya
‘Yan takara za su kammala yakin neman zabe a CAR
A yau Litinin ake kammala yakin neman zaben shugaban kasa da na Yan Majalisu a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashin hankali.
Wallafawa ranar:
Talla
A ranar Laraba ne 30 ga watan Disemba al’ummar kasar za su kada kuri’a domin zaben sabon shugaba.
‘Yan takaran shugaban kasa 30 ke fafatawa don neman shugabancin kasar da ta fada cikin tashin hankalin kabilanci da addini shekaru uku da suka gabata.
Kungiyar kasashen Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga al’ummar kasar su kai zuciya nesa wajen ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu