Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

An dage zaben Afrika ta tsakiya zuwa 30 ga Disemba

Gwamnatin rikon kwarya a kasar Afrika ta tsakiya ta dage zaben kasar da aka shirya yi ranar Lahadin zuwa ranar 30 ga watan Disemba. Gwamnatin tace an dage zaben ne na shugaban kasa da na ‘Yan majalisu domin kammala shirin zaben musamman aikin horar da malaman zabe.

Shugaban jamhuriyar Afrika ta Tsakiya mai rikon kwarya Catherine Samba-Panza
Shugaban jamhuriyar Afrika ta Tsakiya mai rikon kwarya Catherine Samba-Panza AFP PHOTO / PACOME PABANDJI
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da matakin dage zaben, musamman a kasar da ke cikin yanayi na rashin tsaro.

Sai dai kuma dole sai kotun kasar ta amince da matakin dage zaben.

Ana ganin Zaben a matsayi mataki da zai kawo karshen rikicin kasar inda mutane da dama suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.