‘Yan Afrika ta tsakiya sun amince da sabon kundin tsarin mulki
Sakamakon Zaben raba gardama a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya nuna cewar kashi 93 na al’ummar kasar sun amince da sabon kundin tsarin mulkin da aka rubuta.
Wallafawa ranar:
Sabon kundin ya kunshi wa’adin shugabancin kasar sau biyu da yaki da cin hanci da rashawa da murkushe masu dauke da makamai.
Sakamakon zaben zai dada karfafa shirin zaben shugaban kasar da na ‘Yan Majalisu da za a gudanar a cewar shugaban hukumar zabe Marie Madeleine N’Kouet Hoornet.
Yanzu haka ‘Yan takara 30 ne suka kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Lahadi bayan al’ummar kasar sun amince da sabon kundin tsarin mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu