Masar ta kashe ‘Yan ta’adda 24 a yankin Sinai
Rundunar Sojin kasar Masar tace ta kashe ‘yan ta’adda 24 kusa da inda jirgin saman kasar Russia yayi hadari dauke da fasinjoji 224. Sanarwar sojin tace an kashe mutanen ne a cikin wasu tsaunukan da suka samu mafaka, yayin da aka kama wasu 8 daga cikin su.
Wallafawa ranar:
A yau Talata, Rasha tace ‘Yan ta’adda ne suka tarwatse jirgin fasinjanta a yankin Sinai. Shugaban kasar Vladimir Putin ya sha alwashin gano ‘yan ta’addan tare da murkushe.
Yankin na Sinai na daga cikin inda ake samun tashin hankali a cikin kasar, musamman hare haren ‘Yan ta’ada masu alaka da kungiyar IS da ke da'awar jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu