Isa ga babban shafi
Kamaru

Kungiyar ‘Yan jaridu ta nemi a saki Dan Jaridar Najeriya da Kamaru ta kame

Shugaban Kungiyar ‘Yan Jaridun kasar Kamaru Charles Ndi Chia da kungiyar ‘Yan Jaridu da duniya sun yi allawadai da yadda hukumomin kasar suka kama wani Dan jaridan Najeriya Samuel Ateba wanda ya je aiki a kasar don sanin halin da ‘yan gudun hijira ke ciki.

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya (Photo : AFP)
Talla

An kama Mr Ateba wanda dan assalin Kamaru ne ranar juma’a a sansanin ‘yan gudun hijirar Najeriya da ke Minnawo inda aka tasa keyarsa zuwa Makolo da ke Arewa mai nisa.

Rahotanni sun ce hukumomin Kamaru na zargin Dan Jaridar ne yi wa Mayakan Boko Haram liken asiri.

Shugaban kungiyar ‘Yan Jaridu ta duniya y ace babu wata doka da ta haramta wa Dan Jarida shiga sansanin ‘Yan gudun hijira domin dauko rahoto.

Haka ma Hukumar Radio France Internationale ta bukaci hukumomin Kamaru su bai wa lauyan wakilin Sashen Hausa Ahmed Abba damar ganawa da shi bayan an tsare shi na tsawon wata guda ba tare da ba shi damar ganawa da wani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.