Isa ga babban shafi
Kamaru

Boko haram ta kashe mutane 10 a Kamaru

Mayakan Boko Haram sun kashe akalla mutane 10, da suka hada da sojoji biyu, tare da cinna wa gidaje wuta a wani garin da ke arewacin kasar Kamaru.

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane da dama a arewacin Kamaru
Mayakan Boko Haram sun kashe mutane da dama a arewacin Kamaru AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Wata majiyar tsaro a yankin tace bayan harin na garin Blame, da ke a yankin tafkin Chadi iyakar Najeriya da kasar ta Kamaru, ‘yan ta’addan sun janye daga yankin.

Najeriya da ke makwabta da kasashen Chadi, Kamaru da Nijar dukkaninsu da ke fama da matsalar ‘yan Boko Haram sun kaddamar da rundunar hadin gwiwar domin murkushe mayakan.

Yanzu haka Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba Manyan hafsoshin tsaron Kasar watanni uku su murkushe Kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da barazana ga kasashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.