Deby na Chadi ya ce Boko Haram ta nada sabon Shugaba Muhammad Dawud
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ce sun nakkasa Boko Haram kuma suna dab da murkushe ayyukan mayakan kafin karshen shekarar nan. Shugaban kuma ya ce Mayakan sun nada sabon shugaba mai suna Muhammad Dawud.
Wallafawa ranar:
A hirarsa da RFI sashen Faransanci, Shugaba Deby ya ce yana da tabbacin za su iya kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram kafin karshen wannan shekara, domin a yanzu wadansu tisraru kawai ne suka rage a cikin kungiyar.
Shugaban ya ce sun samu labarin Boko Haram ta nada sabon shugaba mai suna Mahammad Dawud a matsayin wanda ya gaji Abubakar Shekau da ake hasashen an kashe shi bayan an dade ba a ji duriyarsa ba.
Deby ya ce sabon shugaban ne ya bukaci a yi tattaunawar sulhu da gwamnatin Najeriya. Amma Shugaban na Chadi ya ce baya goyon bayan yin sulhu da dan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu