Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta dawo da dokar hukuncin kisa

Kasar Chadi ta sake dawo da dokar zartas da hukuncin kisa, watanni shida bayan soke wannan doka lura da yadda ayyukan ta’addanci ke ci gaba da shafar kasar.

Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby Photo AFP / Bertrand Guay
Talla

Chadi ta dawo da dokar ne domin zartar wa ‘Yan ta’adda da hukuncin kisa.

Chadi kuma ta tsawaita hukunci ga duk wanda aka kama da laifukan da suka shafi ta’addanci zuwa daurin shekaru 20 a gidan yari.

Kudirin dokar ya samu amincewar Majalisar kasar ba hamayya.

Kasar Chadi da rikicin Boko Haram ya shafa na ci gaba da duakar matakan tsaro bayan hare haren kunar bakin wake da aka kai N’Djamena fadar gwamnatin kasar.

Kazalika, hukumomin sun haramta gudanar da barace-barace a cikin manyan birane saboda da yadda ‘yan ta‘adda ke amfani da irin wannan dama domin kai hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.